Zan Dawo A Shirin Dadin Kowa Wasa Farin Girki - Sallau


Assalamu alaikum barkanmu da kasance a cikin shirin labarin kannywood,

Shahararren dan wasan kwaikwayon nan na cikin shirin dadin kowa UMar Muhammad Sani Jigirya wanda akafi sani Da Sallau kowa Naka, yace yana nan zai dawo a cikin shirin dadin kowa wasa farin girki, ko meye dalilinsa na fadawa duniya haka kuma alhali dama a sanshi tun daga farkon shirin.

Ya bayyana hakanne a wata hira d sukai da jaridar northflix ne, bayan an juma ba a ganin sallau a cikin shiri, sai yace.

Dama shi wasa mai dogon zango ya gaji haka yau kaganka a cikin gobe kaga babu kai sakamakon shirin gidajen da akasa sunyi yawa ga kuma bangarori daban daban.

Shin ko akwai ka a cikin shirin dadin kowa wasa farin girki, tambayar da dan jaridar yayi wa jrumin.

Eh ina sa rai dan a yanzu haka anyi sainin dina akan shirin, kaga kenan alamu akwaini a ciki.
Zan Dawo A Shirin Dadin Kowa Wasa Farin Girki - Sallau Zan Dawo A Shirin Dadin Kowa Wasa Farin Girki - Sallau Reviewed by Fim on February 16, 2020 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.