Shahararriyar jarumar kannywood wace tauraruwarta take kan ci wato hadiza gabon ta bayyana fatanta nan da shekara 5 a wata hira da tayi da gidan bbchausa a inda take amsa tambayoyin da gidan yada labaran yake mata.
GA TAMBAYOYIN:-
Shin ko menene Fatanki Nan Da Shekara 5?
Jaraumar ta amsa da cewa, fatana nan da shekara biyar shine Aure, Haihuwa, Arziqi.
Minti Nawa Kike Dauka Kina Kwalliya?
Nan ma jarumar ta sake basu amsa da cewa, Bancika yin kwalliya ba yau dinma nayine don za'ai hira dani.
Wanene Saurayinki A Kannywood?
Tacewa mai tambayar, karka kashemin kasuwa mana, duk yan uwana ne a kannywood.
Wane Rade-Radi ake yadawa akanki?
Tace, Tagirma ta tsufa batai aureba, bataso tai aure, abubuwa da yawa, amma dai yana daya daga cikin abubuwan da ake fada.
Ya kikeji idan an zageki?
Wani lokaci na kanyi dariya, wani lokaci na kanyi kuka, sannan wani lokaci na kan rama.
Kayanki Kala Nawa Ne?
Ban sani ba.
Wane Kalan Kaya kikafi so?
Kayan da nafi so nafi sa dogayen riguna, Sannan nafi son atamfa.
Rera Mana Wakar Fim Din?
Kyan tafiya dawowa, wani abu haka.
Wane fim dinki ne sunanki ya bi ki?
Yawanci inaga kamar yar maye ta dan abun nan, amma har yanzu zakaji ance hadiza gabon, kamar hadiza gaban din ya danne wasu sunayen fina-finan da nayi.
Fadi Abubuwa Uku Game Da Ke?
Ni Mutuniyar kirki ce, tara bata cika goma ba, dan adama dama ajizi ne.
Da wa kika fi so a hadaki a Fim?
Ya danganta da furodusa da daukar da akayi, gaskiya bani da zabi, kawai ni abinda nake gani shine wanda aka hadaka dashi kayi kokari kaga cewa ka kawo abinda suke nema ka kawo ko fiye da haka.
Wannan Shine hirar tasu a Takaice
Shin Ko Kunsan Menene Fatan Hadiza Gabon Nan Da Shekara 5?
Reviewed by Fim
on
February 13, 2020
Rating:
No comments: