Annabi Ya Roka Mana Kar Allah Ya Kamamu Da Laifi Sai Anje Lahira -Shiyasa nake Wakar Batsa

556tgfv

A watan da ya gabata ne dai haruna chizo bahaushe ma zaunin kasar jamani   wanda yayi kaurin suna a shafukan yanar gizo musamman a wasan barkwanci  da yake gami da raye raye wanda yanzu kuma ya tsuduma ka'in da  na'in a wakokin hausa.

Amma yanzu haruna cizo yazo da sabon salon  da ya sa daukacin mutane tir da Allah wadai da wannan tsarin duk da dai akwai daidai ku da kuke goyon bayansa  a wannan tsarin ba komai bane face tsari na wakar batsa muraran ba tare da sakayawa ko amfani da kalmomi na badda bani ba aa ainihin kalmomin batsar yake kira a cikin wakokin nasa.

Tun a satin da ya saki waka wanda ya yiwa lakani da sunan Al'aura ya fara shan korafi inda har sukayi ta masayar kalamai da wani  mai amfani da kafar instagram suna young ustaz.

A karshe dai gidan radio sarewa na kasa da kasa  sun sami zantawa da haruna cizo inda  ma'aikaciyar tasu ta same shi har inda yake a kasar jamani inda tayi masa tambaya kan dalilin da yasa yake yin wakokin batsa mai makon yin na fadakarwa haruna ya kada baki ya jawo aya ya fassara inda ya ke kafa  hujja da cewa ma'aiki (S.A..W) ya roka mana kar Allah ya kama kowa da laifi har sai anje lahira.

Ko da yake annan tsakure ne akan hirar da akayi dashi amma wannan ya tabbatar da cewa haruna na yana nan akan bakarsa bai kuma saduda da wannan salon nasa ba bashi kuma da niyar canza salo.

To Allah ya kyauta.
Annabi Ya Roka Mana Kar Allah Ya Kamamu Da Laifi Sai Anje Lahira -Shiyasa nake Wakar Batsa Annabi Ya Roka Mana Kar Allah Ya Kamamu Da Laifi Sai Anje Lahira -Shiyasa nake Wakar Batsa Reviewed by Fim on February 17, 2020 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.